Bidiyo: Yadda bam ɗin Yaƙin Duniya Na Biyu ya tashi a ƙoƙarin cire shi
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Wani bam mafi girma na Yaƙin Duniya Na Biyu da aka gano a Poland ya fashe a yayin da ake ƙoƙarin cire shi.
Sai dai an yi matukar sa'a babu wanda ya mutu ko ya ji rauni.
Rundunar sojin ruwan Birtaniya ce ta jefa bam ɗin a teku a wani hari da aka kai a shekarar 1945 wanda ya sa jirgin ruwan Jamus ya nutse.