Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sule Lamido: Duk soyayyata da Buhari ba zan yi masa addu'a ba
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Mutane da dama na ganin Najeriya ta cimma dumbin nasarori a tsawon shekara sittin na rayuwarta, yayin da wasu ke ganin ci gaban da ƙasar ta samu ya zuwa yanzu bai taka kara ya karya ba idan an kwatanta da sauran sa'o'inta a duniya.
Daya daga jagororin hamayya a Najeriya 'yan jam'iyyar PDP Alhaji Sule Lamido ya ce kasar ta cimma wasu nasarori a cikin shekaru sittin, to amma ya ce nasarorin ba su kai yadda ya kamata ba.
Tsohon gwamnan na jihar Jigawa kuma tsohon ministan harkokin wajen Najeriya ya kuma yi tsokaci kan salon mulkin Shugaba Buhari na jam'iyyar APC.