Matar da ke sayen iskar da take shaƙa kullum ta N5,000 a Najeriya

Baiwar Allah wadda mai gidanta ya rabu da ita saboda lalurar ciwon, na fadi-tashin biya wa yaranta biyar kudin makaranta da kuma kudin haya baya ga naira 5,500 na sayen iskar Oxygen kullum.