Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yar Kenya ta lashe kyautar Komla Dumor ta 2020
Latsa hoton sama don kallon bidiyon Victoria Rubadiri
Ƴar jaridar Kenya da ke binciken ƙwaƙwaf, Victoria Rubadiri ta lashe lambar yabo ta Komla Dumor ta BBC ta shekarar 2020.
Rubadiri mai gabatar da shirye-shirye ce a kafar yada labarai ta Citizen TV a kasar Kenya.
Kwararriyar 'yar jarida ce mai masaniya kan al'amuran Gabashin Afirka kuma ta yi hira da manyan mutane a bangaren siyasa da lamuran yau da kullum.
An kirkiri kyautar ce domin girmama Komla Dumor, wani mai gabatar da shirye-shirye a kafar BBC wanda ya yi rasuwar fuji'a yana da shekara 41 a 2014.
Rubadiri ce ta shida a jerin wadanda suka lashe kyautar, inda ta bi sahun Solomon Serwanjja da Waihiga Mwaura da Amina Yuguda da Didi Akinyelure da kuma Nancy Kacungira. Ita ce 'yar Kenya ta biyu da ta lashe ta.
Za ta fara daukar horo na wata uku tare da BBC ta hanyar halartar darusa a Sashen Koyon Aikin Jarida kafin ta fara aiki da tawagar da ke shirya labarai ta talabijin da rediyo da kuma intanet.
"Komla dan jarida ne masanin fannoni da dama, wanda salonsa mai ban-kaye yake da dadi tare da karfafa mai sauraro. Yana burge ni ta yadda yake iya rike masu sauraronsa ta hanyar bayar da labarai na gaskiya," a cewar Rubadiri.
"Na kagu na koyi sabbin abubuwa a BBC da za su sa masu saurarona a gida da waje su ci gaba da kasancewa tare da ni ta kowacce kafa," in ji ta.
Ta burge alkalan gasar da iya maganarta da kuma son bayar da labaran Afirka ta kafar yada labarai ta zamani da kuma wadda aka saba.
"Muna murna da samun Rubadiri domin ta kawo mana kwarewa da salonta a BBC," in ji Jamie Angus, Shugaban BBC na sashen yada labarai ga kasashen duniya (BBC World Service Group).
Ya kara da cewa: "Komla na da kwarewar bayar da labarai daga Afirka ta hanyar labarta su cikin fahimta. Muna jiran ganin kwarewar Victoria."