Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa na da hannu a wani harin sama da aka kai a Libya
BBC ta samu wasu sabbin bayanai da ke nuna cewa wani jirgi mara matuƙi mallakar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya kashe wasu masu koyon aikin soja 26 a Libya a ranar 20 ga watan Janairu.
Sannan ta tura jirage maras matuƙi da wasu kayayyakin soji ga abokanta na Libya; kana Masar ta ƙyale Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta yi amfani da sansanonin mayaƙan samanta da ke kusa da iyakar Libya.