Rikicin Bauchi: Yadda DPO ya 'kashe' matasa da taɓarya a caji ofis
Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Mutuwar matasan biyu ta faru ne sakamakon dukan da jami'in ɗan sanda ya yi musu su uku kan zargin satar kaji a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Ana zargin lamarin ya faru ne bayan ɗan sandan ya yi wa wasu matasa uku duka da taɓarya a caji ofis.
Ɗaya daga cikinsu ya tsira da karaya iri-iri. Ana zargin matasan ne da sace kaji na wani mutum a birnin Bauchi.
Kungiyoyin kare hakkin ɗan Adam kamar Human Rights da Amnesty International da ma wasu kungiyoyi na cikin gida sun sha zargin jami'an tsaron Najeriya da keta hakkin bil Adama ciki har da kisa ba tare da shari'a ba da azabtarwa da sauransu.
Rundunar 'yan sanda a jihar ta ce ta kafa kwamiti domin binciken azabtarwar da kuma kisan matasan da ake zargin ɗan sandan ya yi.
Abdulwahab Bello, shi ne matashi daya tilo da ya tsira da ransa daga azabtarwar da ake zargin jami'i ɗan sandan ya yi masu. Abokansa biyu sun mutu sanadiyyar duka da taɓarya da ake zargin wani babban jami'in dan sanda ya yi masu a caji ofis.
Abdulwahab ya ce shi magini ne, amma da abokansa biyu suka zo da kaji guda bakwai, ya raka su kasuwa suka sayar da su, amma daga bisani sai aka ce ana zargin kajin na sata ne.
Tuni dai wannan al'amari ya tunzura wasu 'yan Najeriya inda har suka dinga mayar da martani a shafukan sada zumunta da muhawara.
Barista Bulama Bukarti wani fitaccen lauyan kare hakkin dan adama ne kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, ya wallafa a shafinsa na tuwita cewa:
''A lokacin da kake tunanin al'amari ba zai rincaɓe ba, sai a ce maka ɗan dakata. Da safiyar nan (ranar Asabar) BBC Hausa suka yi wani labari kan yadda wani DPO a Bauchi ya zabtar da wasu mutum biyu har suka MUTU yayin da na ukun ya tsira da karaya BIYAR kan zargin satar kaji.
Shi ma Hussain Gimba Galadima ya wallafa cewa:
''Kusan wata guda kenan da faruwar lamarin amma har yanzu 'yan sanda ba su fitar da sakamakon binciken da kwamishinan 'yan sanda ya sa a yi ba, don haka ina kira ga Gwamna Bala Muhammad da shi ma ya kafa nasa kwamitin bbinciken.''
Abdulmumin Abdulwakil kuwa cewa ya yi: ''Abu mafi muni shi ne har yanzu kwamitin da hukumar 'yan sanda ta kafa bai tuhumi DPO din kan abin da ya aikata ba da kuma bincike kan wannan mummunan aikin, hakan zai bai wa mutanen da aka bai wa amanar kare rayuka da dukiyoyin jama'a damar sakeaikata irin wannan laifin.