Yadda na samu takardar NCE da kudin jari bola

Ku latsa hoton da ke sama domin kallon labarin Isa Baban Bola

Labarin Isa Muhammad, matashi dan asalin jihar Katsina wanda ya bar garinsu ya je babban birnin Najeriya, Abuja domin neman kudi, yana da kwarara gwiwa.

Baban bola kamar yadda aka fi sanin masu sana'a irin ta Isa, ya je Abuja bayan mahaifan nasa sun rasu abin da ya tilasta masa ficewa daga makarantar sanadare.

Amma jajircewa irin ta Isa Muhammad wanda yanzu shekarunsa 25 ne ta sa yanzu haka yana da takardar shaidar koyarwa ta NCE.

Burin Isa kuma a nan gaba shi ne ya mallaki takardar shaidar digiri.

Bidiyo: Chukwuemeka Anyika

Mai tsarawa: Usman Minjibir