Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jariran da ke shan madarar shanu 'za su tashi da halayyar saniya'
Latsa alamar lasifika da ke sama don sauraren hira da Dr. Mandara:
Masana harkoki lafiya sun gargadi mata su guji bai wa jarirai madarar shanu ta gwangwani domin jariran za su iya daukar halayya irinta saniya.
Dr Mairo Mandara, wata kwararriyar likita a fannin lafiyar iyali da cututtukan da suka shafi mata da kananan yara, ta shaida wa BBC cewa yana da matukar muhimmanci iyaye su mayar da hankali wurin bai wa jariransu nono tun daga ranar farko.
"Shi nonon uwa yana tare da wadansu sinadari da an yi su ne musaman don jaririn; wato akwai sinadarin lafiya, akwai sinadaran da ba su bari wasu cututtuka su kama yaron, da abubuwan gina jikin yaron da dukkan abubuwan gia kwakwalwar yaron."
Likitar ta kara da cewa daga ranar farko zuwa wata shida ake gina kwakwarlwar jariri shi ya sa yake da matukar amfani a ba shi nonon uwa zalla.
Ta jaddada cewa bayar da nonon uwa zalla yana taimakawa ita kanta mai jego wajen inganta lafiyar da ta jariri tana mai cewa nonon madarar gwangwani yana da illa sosai.
A cewarta: "Madarar gwangwani nonon saniya ne' idan ko aka ba jariri nonon saniya, za ka ga yakan iya tashi da halin shanu, sai ka ga yaro ba shi da nutsunawa.Jaririn da ya sha nonon uwarsa yana sa masa tausayi, yana sa masa kauna."
Dr Mandara tana wannan bayani ne a yayin da Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce annobar korona ta kara fito da bukatar daukar kwararan matakan shayar da jarirai nonon uwa zalla fili.
Cikin wata sanarwa asusun na UNICEF ya yi kira ga gwamnatoci da su fito da wasu hanyoyi da za su taimakawa mata wajen samun shawarwari kan muhimmancin shayar da yara nono.