Zan nemi ganin Shugaba Buhari kan matsalar tsaro - Gudaji Kazaure

GUDAJIKAZAUREFACEBOOK

Asalin hoton, GUDAJIKAZAUREFACEBOOK

Bayanan hoto, Gudaji Kazaure ya ce matsalar tsaron ce ta hana mutane ganin ayyukan da gwamnatinsu ke aiwatarwa a Najeriya

Wani fitaccen ɗan majalisar wakilai daga arewacin Najeriya, ya faɗa wa BBC cewa zai nemi ganawa da shugaba Buhari don bayyana masa halin taɓarɓarewar tsaro da wasu yankunan ƙasar ke ciki.

Honorabul Gudaji Kazaure ya ce yana da hujjoji da wasu ƙwararan shawarwari da zai bai wa shugaban kuma ya yi imani za su yi amfani wajen shawo kan matsalar tsaron da ake fama da shi.

A zantawarsa ta shafin BBC Hausa Faceboo, kan matsayinsa game da cutar korona wadda ta addabi duniya, Gudaji Kazaure ya koka kan "yadda ake kurara cutar, (don kuwa) ba ta kai yadda ake kai ta ba".

Wasu sun yi imani ɗan majalisar na amayar da ra'ayin 'yan Najeriya da dama ne, inda suke zargin cewa mahukuntan ƙasar na bai wa annobar korona kulawar da ta fi sauran matsalolin ƙasar musamman ma taɓarɓarewar tsaro.

Dan majalisar wakilan ya ce "Ka duba ka ga yadda aka bai wa wannan cutar muhimmanci a kowacce jiha, a kowacce ƙaramar hukuma ta Najeriya, aka fid da maƙudan kuɗi. Amma mutum nawa ta kashe?"

Gwamnatin Najeriya ta rufe kusan duk harkokin tattalin arziƙin ƙasar tsawon makwanni, bayan ɓullar annobar korona ranar 27 ga watan Fabrairu.

Kuma har yanzu, ba a buɗe makarantu da zirga-zirga tsakanin jihohin ƙasar da kuma harkokin sufurin jiragen sama ba, yayin da yawan masu cutar ya ƙaru zuwa sama da 12,500.

An kuma ba da rahoton cutar ya zuwa yanzu ta kashe mutum 354 a Najeriya.

Gudaji Kazaure ya ce ya yi imani kafin cutar korona ta kashe mutum ɗaya a Najeriya, "'yan bandit ('yan fashin daji) sun kashe mutum 100".

"Ka duba ka ga rannan a Sakkwato, mutum 70 fa rana ɗaya suka kashe. A ina korona ta kashe waɗannan mutane cikin kwana ɗaya? Ɗan majalisar ya tambaya.

A cewarsa irin kashe-kashen da 'yan fashin daji suke yi su ne suka fi damunsa a kan cutar korona wadda yake ganin an fi mayar da hankali kanta a ƙasar.

Kalaman Gudaji Kazaure na zuwa ne kwana ɗaya bayan wata sanarwar shugaban ƙasar wadda a ciki Buhari ke kira ga 'yan fashin daji su ajiye makamai ko kuma su kuka da kansu.

Dan majalisar wakilan Nijeriya Hon Muhammad Gudaji Kazaure

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto, ''Ba na shakkar tsayawa in yi magana a zauren majalisar don kawai saboda kada in yi kuskuren Turanci.''

Kiran ya zo ne 'yan kwanaki bayan 'yan fashin sun hallaka mutane da dama a mahaifarsa ta Katsina cikinsu har da hakimin 'Yan Tumaki, Alhaji Atiku Mai Dabino, da shugaban Jam'iyyar APC na karamar hukumar Batsari Alhaji Abdulhamid Sani Duburawa.

Shugaban ƙasar ya kuma gana da Gwamna Aminu Bello Masari ranar Alhamis don tattaunawa kan matsalar tsaro da ta addabi yankin arewa maso yammaci.

Buhari dai ya nanata ƙudurinsa na sake ƙaddamar da farmaki kan 'yan fashin daji a jihohin Zamfara da Sokoto da Neja da Katsina da kuma Kaduna.

A ƙarshen watan jiya ma sai da 'yan fashin daji suka auka wa wasu ƙauyuka a yankin Sabon Birnin Gobir na jihar Sokoto inda suka kashe mutane fiye da 60.

Shaidu sun ce maharan sun shafe tsawon sa'o'i suna ta'adi a kauyukan ba tare da wani jami'in tsaro ya ko tunkare su ba.

Honorabul Kazaure ya ce irin wannan kisa ba-ji-ba-gani da 'yan fashin daji suke yi a wasu sassan arewacin ƙasar su ne suka dame shi.

A cewarsa: "A yanzu ne nake ƙoƙari, ko yau ko gobe in nemi izinin yadda zan je in gan shi". Ya ce so da ƙaunar da ke tsakaninsu ba za ta hana shi faɗa wa shugaban ƙasar gaskiya ba.

An kuma tambaye shi ko har ga Allah ya gamsu da yadda Shugaba Buhari ya riƙe Najeriya a tsawon shekara biyar da ya yi a kan mulki? Gudaji Kazaure dai bai yi ba da amsa kai tsaye ba.

Ya ce abin da yake so mutane su fahimta shi ne, "ban san me ya sa ba, yana daga cikin kuma abin da zan gaya mishi. Ya fito ya gaya wa al'umma gaskiyar al'amari".

"Ba wai ya kasa ba ne, a'a! Kuɗin da za a yi wa al'umma aiki a Najeriya, wallahi babu su," in ji Gudaji Kazaure.