Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Yadda mutanen Wuhan suka ci galabar annobar
Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Yayin da coronavirus ke ci gaba da yaduwa a sassan duniya tana kashe mutane, mutanen Wuhan, birnin da cutar ta fara barkewa a fadin duniya sun bayar da shawarwari ga mutanen duniya.
Wasu daga ciki sun bayyana yadda zama a gida ya zama alheri a gare su da birnin nasu.
Sun kuma bayyana yadda suka yi rayuwarsu da yadda suka ci galabar annobar.