Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kalli binciken BBC kan illar safarar icen Madobiya a Afirka
Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon
Wani binciken sashen BBC Africa Eye, ya bankado yadda bukatar itacen Madobiya a kasar China ke haddasa lalacewar muhalli a yammacin Afirka.
A kiyashi, kasar Gambiya kawai ta fitar da sama da tan 600,000 a tun daga 2017 zuwa yanzu.
Masu safarar itacen na kiran Madobiya da "Zinariyar Daji" domin irin kudaden da suke samu idan suka sayar da icen.