Ritayar Bulkachuwa: Akan yi wa wadanda aka yi wa fyade rashin adalci
Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon
Shugabar kotun daukaka kara a Najeriya Mai Shari'a Zainab Bulkachuwa mai murabus, ta ce wasu lokuta akan yi wa wadanda aka yi wa fyade rashin adalci a kotunan Najeriya.
Mai shari'ar ta bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da ta yi da BBC gabanin barin ta aiki.
A ranar 6 ga watan Maris ne mai shari'ar ta yi ritaya bayan da ta cika shekara 70 a duniya, kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
Kuma Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da nadin Mai shari'a M.B. Dongban Mensem a matsayin mukaddashiyar shugabar kotun daukaka karar kasar.
Bidiyo: Abdulbaki Jari
Tsarawa: Halima Umar Saleh