Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Daga Titunanmu: Shin farin jinin Buhari na karuwa ko raguwa?
Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Daga Titunanmu: A wannan makon mun fita titunan Abuja inda muka tambayi mutane ra'ayoyinsu game da farin jinin shugaban kasar.
A makon da ya gabata ne a birnin Maiduguri a ka yi wa shugaban kasar ihun a lokacin da je yi wa mutanen jihar jaje game da harin da Boko Haram ta kai a Auno wanda ya kashe mutane da dama.
Shugaban kasar na daga cikin shugabannin Najeriya masu farin jini sosai, wannan ne ya sanya ya kada shugaban kasa mai ci a wancan lokacin Goodluck Jonathan inda ya haye mulki a 2015.