Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kama matar da ta daba wa mijinta wuka a Katsina
Ku latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron SP Gambo Isa.
Rundunar 'yan sandan jihar Katsina a Najeriya ta tabbatar da mutuwar wani mutum magidanci da ake zargin matarsa ce ta daba masa wuka a jihar katsina da ke arewacin kasar.
Kakakin rundunar 'yan sandan SP Gambo Isa ya shaida wa BBC cewa suna gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da ya faru.
Matar da ake zargin ta fito ne daga kauyen tashar DanJanku da ke karamar hukumar Malumfashi.