Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
...Daga bakin mai ita tare da Dan Azumi Baba
Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Daga bakin mai ita wani shiri na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zallah.
A wannan kashi na 12, shirin ya tattauna da Dan Azumi Baba Chediyar 'Yan Gurasa, wani fitaccen mai bayar da umarni a fina-finan Hausa, kuma mai fitowa da sunan Kamaye a wani shirin na talbijin na Dadin Kowa.
A cikin hirar, ya bayyana abubuwa da yawa da suka shafi rayuwarsa da za su saku dariya da al'ajabi.
Bidiyo: Fatima Othman