'Tsarin karba-karba ya saba kundin mulkin Najeriya'

Ku latsa alamar lasifika da ke sama domin sauraron farfesa Ibrahim Jibril

A Najeriya, an fara ka-ce-na-ce kan batun babban zaben kasar na shekara ta 2023, wata bakwai kacal bayan rantsar da Shugaba mai ci a kan karagar mulkin kasar.

Zaben dai na da matukar muhimmanci, don kuwa a lokacin ne za a gane ko tsarin karba-karba tsakanin sassan kasar shida yana aiki ko kuma bangaren arewaci zai ci gaba da yin kaka-gida kan madafun iko, bayan kammala wa'adi biyu na shugaba Muhammadu Buhari.

Wasu manyan 'yan siyasa a kasar na ganin ya yi wuri a fara cece-kuce game da zaben tun yanzu, yayin da wasu ke ganin ai da safe ake kama fara.

To masharhanta dai na yi wa al'amarin karba-karba kallon wani abu da 'yan kasar suka kirkira ba don yana cikin tsarin mulkin kasar ba.