Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa Amurka da Iran ba sa ga maciji?
Latsa sama domin kallan bidiyon
Mun yi duba kan yadda alaka tsakanin Amurka da Iran ta lalace tun daga 1959 zuwa yanzu.
Wannan na zuwa ne bayan da Amurka ta kashe babban kwamandan rundunar Quds a garin Bagadaza.
Amurka ta bayyana cewa ta kashe shi ne saboda kokarin da yake yi na shirya kisan sojojinta.
Babban jagoran Musulunci na Iran Ayatollah Khamenei ya sha alwashin daukar fansa a kan kashe kwamandan.