...Daga bakin mai ita tare da Ado Gwanja: 'Mahaifina ne mai shayin Sarkin Kano'

Latsa hoton da ke sama domin kallo da jin abin da dan fim din ke fada.

Daga bakin mai ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zallah.

A wannan kashi na biyar, fitaccen mawaki kuma dan wasan fina-finan Hausa na Kannywood, Ado Gwanja ne ya amsa tambayoyin da za su sa ku dariya ciki har da cewa "zai yi wuya ya kara aure kasancewar shi 'kan-ta-ce ne.''

Ado Gwanja ya kuma shaida wa BBC irin matar da yake so "ba doguwa ba, ba gajeriya ba kuma ba siririya ba ba mai kiba ba."

Dangane da sana'ar gidansu da ya gada, ya ce "ba don waka ba da watakila yanzu shayi nake sayarwa", saboda a cewarsa mahaifinsa ne mai shayin Sarkin Kano.

"Idan Sarkin kano zai sha shayi sai ya turo wurin mahaifina."

Bidiyo: Fatima Othman

Wasu na baya da za ku so ku gani