Bello Matawalle: Abdulaziz Yari ne ummul aba'isin rikicin Zamfara

Latsa alamar lasifika domin sauraren hirar da Awwal Janyau yayi da Gwamna Bello Matawalle.

Gwamatin jihar Zamfara a arewa maso yammacin kasar da ke ikirarin samun nasara kan matsalar tsaron jihar ta dora laifin sabbin hare-haren da aka kai na baya-bayan nan kan tsohon gwamnan jihar.

Gwamna Bello Muhammad Matawalle wanda ya ce ya yi sulhu da wadanda gwamnatinsa ta ke ganin sun addabi jihar, ya zargi wanda ya gada Abdulaziz Yari da yin zagon kasa ga sha'anin tsaron jihar.

Ya ce tsohon gwamnan yana bakin ciki da zaman lafiyar da aka samu wanda ya kasa magancewa shekaru 8 na mulkinsa.

Kana gwamnan ya yi zargin cewa duk lokacin da Abdulaziz Yari ya ziyarci jihar sai an kai hari kuma ya yi barazanar cewa zai dauki mataki a kan tsohon gwamnan idan aka sake kai hari lokacin da ya shiga jihar.