Ko Abba Gida-Gida na da wata dama kan Ganduje?

Abba Gida-Gida

Kotun daukaka kara da ke zama a Kaduna ta tabbatar wa Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje kujerarsa, inda ta yi watsi da karar da jam'iyyar PDP ta shigar gabanta.

Kotun ta yi watsi ne da ikirari 24 da Abba Kabir da kuma PDP suka gabatar mata.

Tun a ranar 8 ga watan Nuwamba ne kotun ta fara sauraron karar, wadda PDP ta daukaka bayan kotun sauraron kararrakin zabe ta yi watsi da ita a shari'ar da mai Shari'a Halima Shamaki ta jagoranta.

Yayin da yake bayar da bayanai a kotun, Mai Shari'a Tijjani Abubakar ya ce hukuncin da kotun baya ta yanke ya inganta kuma Abdullahi Umar Ganduje ne ya ci zaben.

Hakan yana nufin har yanzu PDP ba ta yi nasara a dukkanin kararrakin da ta shigar ba game da zaben gwamna na 2019.

Wace dama ta rage wa Abba Gida-Gida?

Barista Sulaiman Abbas Magashi, lauya mai zaman kansa a Kano ya shaida wa BBC cewa, Abba Gida-Gida na da damar karshe ta zuwa kotun koli idan bai gamsu da wannan shari'ar ba.

Ya kuma zayyana jadawalin yadda shari'ar za ta kaya kamar haka:

  • Da farko wadanda ba su gamsu da hukuncin kotun daukaka kara ba za su je kotun kolin hujjojin doka na rashin gamsuwa da shari'ar kotun koli.
  • Sannan masu kara za su sake rubuta hujjojin shari'a da ke nuna su ya kamata a bai wa nasara ba abokan hamayyarsu ba.
  • Daga nan kuma sai kotun kolin ta mika wa wadanda ake karar hujjojin doka da na shari'a da masu kara suka shigar.
  • Wadanda ake karar za su rubuto martani kan hujjojin doka da shari'ar da masu kara suka mika wa kotun ta koli.
  • Bayan duk wadanne ne kuma kotun ta koli za ta fitar da ranar zama, inda bangarorin biyu za su bayyana a gaban alkalai domin tattauna hujjojin shari'a da na dokokin.
  • Bayan zaman ne kotu za ta yanke ranar zartar da hukunci.
  • Sai dai kotun na da zabi ta kira masu karar da wadanda ake da kara domin ta karanta musu hukuncin ba tare da bayyana wata rana ba.

Kotun dai na da kwanaki 60 wato watanni biyu ta kammala hukunci, daga ranar da aka shigar da karar gabanta.

Barista Magashi ya ce kamar kotun daukaka kara, ba a gabatar da shaidu a gaban kotun koli.

Me ya faru?

Abba Yusuf, wanda aka fi sani da "Abba gida-gida", ya sha kayi a hannun Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a karashen zaben da aka yi, duk da cewa shi ne kan gaba a zaben farko wanda bai kammala ba.

Ganduje ya ci zaben ne na biyu da tazarar kuri'a 35,637 inda jam'iyyarsa ta APC ta samu kuri'a 45,876 yayin da PDP ta samu 10,239.

Idan aka hada sakamakon zaben na farko da na biyu, jimilla APC ta samu kuri'a 1,033,695, yayin da PDP ta samu jimilla 1,024,713. Hakan na nufin Ganduje ya ci zaben ne da tazarar kuri'a 8,982.

Sai dai masu sa ido na gida da waje sun soki yadda aka gudanar da karashen zaben suna masu cewa an tafka magudi, zargin da jam'iyyar APC da kuma hukumar zabe suka musanta.

Ganduje