Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hikayata 2019: Saurari karatun labarin 'A Juri Zuwa Rafi' da ya zo na uku
Latsa alamar lasifikar da ke sama ku sha labari
A karshen watan Oktoba ne gidan yada labarai na BBC Hausa ya karrama matan da suka lashe Gasar Hikayata da aka gudanar kan kagaggun labarai karo na hudu na shekarar 2019.
Jamila Babayo ce ta zo ta uku inda aka ba ta lambar yabo da kuma kyautar $500.
Kuma a wannan makon mun kawo muku labarinta wato 'A Juri Zuwa Rafi', wanda ta karanta da bakinta, kamar yadda aka ce waka a bakin mai ita ta fi dadi.