Hikayata 2019: Saurari labarin 'Maraici' da ya zo na daya

Latsa alamar lasifikar da ke sama ku sha labari

A karshen watan Oktoba ne gidan yada labarai na BBC Hausa ya karrama matan da suka lashe Gasar Hikayata da aka gudanar kan kagaggun labarai karo na hudu na shekarar 2019.

Safiyya Ahmad ce ta zo ta daya inda aka ba ta lambar yabo da kuma kyautar $2,000.

Kuma a wannan makon mun kawo muku labarinta wato 'Maraici', wanda ta karanta da bakinta, kamar yadda aka ce waka a bakin mai ita ta fi dadi.