Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gobara ta tashi a kasuwar Balogun ta Lagos
Ku latsa hoton sama don kallon bidiyon:
Gobara ta tashi a babbar kasuwar Balogun da ke birnin Ikko na jihar Legas a kudu maso yammacin Najeriya.
Wutar ta tashi ne a wasu shaguna da ke gefen kasuwar inda ta kona shaguna da dama da kuma wuraren ajiyar kayayyaki.
Hukumar kare afkuwar hadurra ta jihar Legas LASEMA ta ce a yanzu haka tana wajen tare da 'yan kwana-kwana suna ta kokarin kashe wutar da kuma tabbatar da zaman lafiya a wajen.
LASEMA da kuma hukumar kashe gobara da hukumomin tsaro na jihar suna wajen don tabbatar da cewa an shawo kan wutar.
Sun kuma ajiye lifta a waje don wutar tana ci ne daga bene hawa na shida na wani ginin rukunin shaguna da ke cikin kasuwar ta Balogun.