Matar da ta bude asibitin kyauta ga masu cutar sikila
Ku latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Hajiya Badiyya Inuwa ta haifi masu fama da sikila biyu, daya ya rasu shekaru 14 da suka wuce sanadiyyar cutar.
Hakan ya sa ta bude wata cibiya a Kaduna wadda ke taimakawa talakawa sikiloli da magunguna da kuma fadakarwa.
A yanzu haka, cibiyar tana taimakawa kimanin mutum 4000.
Bidiyo: Fatima Othman