Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Najeriya ta hana bakin haure 1,000 shiga kasar ta kan iyaka
Ku latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron hirar Babandede da Ibrahim Isah:
Hukumar kula da shige da fice a Najeriya ta ce ta yi nasarar hana fiye da bakin haure mutum 1,000 shiga kasar 'yan makwanni bayan rufe iyakokin kasar na kan tudu ciki har da mutanen da suka fito daga nahiyar Asiya.
A cewar hukumar, aikin hadin-gwiwar da hukumar kwastam da kuma sojoji da sauran jami'an tsaro wajen sa ido a kan iyakokin kasar na taimakawa wajen dakile ta'addanci.
A tattaunwarsu da BBC, shugaban hukumar shige da ficen, Muhammad Babandede ya ce Najeriya ta bayar da wa'adi ga wadanda suka shiga kasar ba bisa ka'ida ba su je su yi rijista nan da farkon shekara mai zuwa.
Amma a hirar ya fara ne da fayyace matakin rufe iyakokin Najeriyar da aka yi.