Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bidiyo: Yadda gidan Mari yake a Daura
Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta ce ta rufe wani gidan mari na Malam Bello Mai Almajirai a yankin Daura, inda ta ce an sanya fiye da mutum 360 cikin wani mummunan hali da azabtarwa tsawon shekaru.
Wannan ne gidan da ake zargin ana azabtar da mutane na biyu da hukumomi suka ce sun gano kasa da wata guda a arewacin Najeriya.