Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dattijan Kano sun koka kan satar yara
Ku latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron cikakkiyar hirar BBC da Ado Kurawa:
Wata kungiyar dattawa masu kishin jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Bashir Othman Tofa ta koka kan satar yara da ake yi a jihar ana kai su kudancin kasar.
Wannan kira na zuwa ne bayan da a ranar Juma'ar da ta gabata ne rudunar 'yan sandan jihar ta yi holin wasu mutane shida da take zargin su da sace wasu yara tara tare da siyar dasu a garin Onitsha da ke jihar Anambra, tare da sauya musu addini.
Kungiyar ta bayyana ra'ayinta kan wannan batu ne ta bakin mataimakin shugaban kwamitin yada labarai na kungiyar Mallam Ibrahim Ado Kurawa.
A hirarsa da BBC Hausa, Ado Kurawan ya ce akwai bukatar gwamnatin jihar Kano ta hada kai da ta jihar Anambra don nemo sauran yaran da su ma iyayensu ke kukan bacewarsu lokaci mai tsayi ba a gansu ba har yanzu.