Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matan Iran sun fara zuwa kallon kwallo
Matan a Iran sun samu damar shiga filayen wasannin kwallon kafa domin yin kallo.
Wannan ya zo ne bayan da kungiyar kwallon kafa ta duniya ta yi barazana ga kasar cewa idan ba ta bai wa matan dama ba za ta dakatar da ita.
Wannan shi ne karo na farko a cikin shekaru sama da 40 tun bayan juyin-juya hali na Islama wanda aka yi a kasar a 1979.