Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda wanda ya lashe kyautar Komla Dumor ya ji
Latsa hoton da ke sama don kallon cikakken bidiyon
Serwanjja yana gabatar da labarai a gidan talbijin na kasar Uganda wato NBS TV, inda yake hira da baki da dama a shirin nasa.
A wannan bidiyon, ya yi bayani kan yadda ya ji yayin da aka sanar da shi cewa shi ya lashe wannan lambar yabon.
An kirkiro wannan kyauta ne domin karrama Komla Dumor wanda mai gabatarwa ne a BBC bayan ya yi mutuwar farad-daya a 2014 yana mai shekara 41
Serwanjja ne dan jarida na biyar da ya lashe kyautar ta Komla bayan Waihiga Mwaura da Amina Yuguda, da Didi Akinyelure da kuma Nancy Kacungira.
Bidiyo: Fatima Othman