Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda cutar Sikila ta hana Aisha aure
Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron hirar
Aisha Bello Yusuf tana dauke da cutar Sikila.
Amosanin jini, wadda aka fi sani da cutar Sikila cuta ce da ake gado daga kwayoyin halittar iyaye, inda suke haduwa su fito ba dai-dai ba, a jikin dan da suka haifa.
kwayar halittar na fitowa da siffar lauje maimakon a kewaye kamar yadda ya dace.
Aisha ta bayyana kalubale da dama da take fuskanta kasancewar ta mai cutar Sikila, ciki hada matsalan yin aure.
Bidiyo: Fatima Othman