Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dan Senegal ya gina wani daji da itatuwa miliyan 152
Wani mutum dan asalin kasar Senegal ya farfado da wani daji ta hanyar shuka itatuwa miliyan 152 domin inganta muhalli.
Haidar el Ali ya bayyana cewa yana yin wadannan shukokin ne "don kauna".
Domin yana da 'ya'ya kuma yana zo ya bar masu wani abu mai kyau ba duniyar hadama ba.
Ya kuma koka a kan cewa dan Adam bai damu ya gane irin illar da rashin shuka itacen ke haifarwa ba.