Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jihohi '30' ambaliyar ruwa za ta shafa a Najeriya
Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon
Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya, Engr. Mustapha Y Maihaja ya bayyana cewa jihohi 30 na fuskantar barazanar ambaliya.
Shugaban wanda ya bayyana cewa mafiya yawan jihohin suna a gefen tekun Neja ne da Benue, kamarsu Kogi da Adamawa da Neja da Benue da Kebbi da sauransu.
Ya bayyana cewa a halin yanzu suna cikin "taraddadi" domin ba a san girman abin sai ya faru.
Shugaban ya bayyana cewa sun fadarkar da mutane a kan haka kuma sun bukaci su sanar da su inda suke bukatar taimako domin a taimaka masu.
Bidiyo: Fatima Othman