Yadda daruruwan mahara suka far wa kauyen Nijar

Maharan sun far wa kauyen Shirge da ke makwabtaka da garin Zurmi na jihar Zamfara a Najeriya suka kashe mutane suka jikkata wasu, sannan suka kwashe kayan abinci da dabbobi.

Maradi
Bayanan hoto, Mutane shida ne aka kashe aka kuma jikkata wasu takwas a wani hari da 'yan bindiga suka kai kauyen Shirge da ke Maradi a jamuhuriyar Nijar ranar Alhamis da yamma. Tuni aka yi jana'izar mutanen da suka riga mu gidan gaskiya.
Mara
Bayanan hoto, 'Yan bindigar sun kuma jikkata mutum takwas a harin, inda suka shafe sa'o'i uku suna cin karensu ba babbaka a kauyen. Mazauna kauyen sun ce maharar sun je tun da karfe hudu har zuwa karfe bakwai na yamma,
Maradi
Bayanan hoto, Mazauna kauyen sun ce maharan da suka farwa garin a babura fiye da 200 sun kona gidaje da dama.
Maradi
Bayanan hoto, Sun kuma kwashe abinci daga rumbuna, sannan suka kona rumbunan ajiyar abincin.
Maradi
Bayanan hoto, Maharan sun kuma kore dabbobi da dama daga kauyen na Shirge, wanda yake da nisan kilomita uku daga garin Zurmi na jihar Zamfara da ke Najeriya.
Maradi
Bayanan hoto, Baya ga gidaje da rumbunan abinci maharan sun kuma kona wasu motoci.
Maradi
Bayanan hoto, Fargabar da mutanen kauyen suka shiga ta sa jama'a musamman mata da yara kaurace wa kauyen.
Maradi
Bayanan hoto, Sai dai gwamnan jihar Maradi Alhaji Zakari Oumarou ya mayar da wasu daga mutanen da suka kaurace, inda ya tabbatar musu da ba su kariya.
Maradi
Bayanan hoto, An kuma ajiye wata tawaga ta sojoji a kauyen domin tabbatar masu da ba su kariya.