Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Adikon Zamani: Me ya sa ma'aurata ke kokarin kashe juna?
Ku latsa lasifikar da ke sama don sauraron cikakken shirin:
Rashin jituwa tsakanin ma'aurata dai ba wani sabon abu bane. Kai ba ma ma'aurata ba, muddin dai ana zama tare toh dole ne fa a saba wa juna, don ko Bahaushe na cewa 'zo mu zauna, zo mu saba'.
Wani bakon al'amari ya bullo a 'yan kwanakin nan wanda ba a saba gani ba a arewacin Najeriya, wato mace ta dauki makami ko makamancinsa ta yi wa maigidanta lahani idan sun samu rashin jituwa.
A baya, idan rigima ta kaure tsakanin mace da mijinta akan kai ga ya kai mata duka har ya yi mata rauni ko ma ya kashe ta.
To sai dai ba a saba ganin matan na ramawa ba.
A watan Nuwamban 2017 ne 'yan sanda suka kama wata mata da zargin soka wa mijinta wuka a gidansu a Abuja.
'Yan sanda dai sun zargi matar, Maryam Sanda da daba wa mijinta Bilyaminu Bello wuka a gidansu da ke unguwar Maitama a Abuja, Najeriya bayan wata hatsaniya da ta shiga tsakaninsu.
Bilyaminu ya rasu bayan zubar da jini dalilin raunukan da ya samu.
Wannan labarin ya bazu kamar wutar daji saboda ba kasafai ake ganin afkuwar irin haka ba musamman ma a arewacin Najeriya.
Bayan wannan, an samu karuwar wasu matan da kokarin kashe mazajensu kamar wata mace a jihar Zamfara dake arewacin Najeriya da 'yan sanda suka ce ta soka wa mijinta kwalba a kirji.
Masu fafutukar kare hakkin dan Adam a fadin duniya dai na ci gaba da yin kamfe don hani ga irin wannan halayyar.
Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa mata a Afirka na fuskantar barazanar cin zarafi.
A Najeriya kawai, kashi 23% na mata ne suka fuskanci cin zarafi daga mazajensu.
To sai dai gashi yanzu matan na rama wannan mataki da mazan ke dauka a kansu.
Babu wasu alkalumma da ke nuna yawan matan da ke rama cin zarafin da mazansu ke masu a Najeriya, amma a 'yan shekarun nan rahotannin da ke fitowa daga sassa daban-daban na kasar sun nuna cewa mata sun fara mayar da martani.
A wannan makon, mun tattauna da marubuciya kuma mai fafutukar kare hakkin mata, Rahama Abdulmajid da dan jarida Umar Muhammad kan wannan batu.