Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda dan shekara 15 ya 'kera' Tifa a Najeriya
Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Hope Emmanuel Frank yaro ne dan shekara 15 daga jihar Akwa Ibom da ke kudu maso kudancin Najeriya.
Hope ya yi amfani da sirinji da kuma ledar karin ruwa ta asibiti domin hada mota mai hakar kasa.
Ya shafe kusan shekara daya kafin ya hada mota mai hakar kasar.
Hope na da burin zama wanda ya fi kowa iya kirkire-kirkire a fadin duniya.