Fafaroma ya sumbaci kafar jagororin Sudan ta Kudu

Fafaroman ya sumbaci kafafun tsofaffin shugabanin kasar Sudan ta Kudu a yayin wata ziyarar ibada da suka kai fadar Vatican ta tsawon kwanaki biyu.

''Ina umartar ka a matsayinka na dan uwana da mu zauna lafiya. Ina bukatarka da zuciyata, don a samu ci gaba,'' in ji Fafaroman mai shekara 82.

Shugaba Salva Kiir, da abokin hamayyarsa tsohon shugaban 'yan tawaye Riek Machar sun yi arangama da juna shekarar a 2013 a lokacin yakin basasa wanda aka yi asarar rayuka kusan 400,000.

Amma sun saka hannu a kan wata yarjejeniyar zaman lafiya a shekarar da ta gabata wanda ya kawo karshen yakin.