Abubuwan da ba ku sani ba game da CP Wakili Singham

Tauraruwar kwamishinan 'yan sandan Kano CP Muhammad Wakili Singam na kara haskawa tun bayan da ya fara aiki a Kano. To sai dai mutane kadan ne suke da masaniya kan rayuwarsa.

A wata hira ta musamman BBC ta tambayi kwamishinan da ake kira Singham, ya bayyana wasu sirrikan rayuwarsa da mafi yawan jama'a ba su sani ba.