Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Buhari ba shi da hannu a abin da ya faru a zaben Kano'
Fadar shugaban Najeriya ta wanke shugaban daga zargin da ake na cewa Shugaba Muhammadu Buhari yana da hannu a abubuwan da suka faru a zaben Kano.
Dumbin mutane da kungiyoyi, sun yi ta bayyana ra'ayoyi daban-daban kan sakamakon zaben gwamnan na Kano, inda wasu suka kalubalanci Shugaba Buhari da yin shiru ga zarge-zargen amfani da 'yan daba da tarzoma musamman a zaben cike-gibin da aka yi.
Wata kungiyar matasan jam'iyyar APC ta Muhammadu Buhari ma ta fito tana kira ga uwar jam'iyyar a kan ta gudanar da bincike da nufin hukunta masu hannu cikin abubuwan da suka faru.
Malam Garba Shehu, shi ne mai magana da yawun shugaba Buhari, ga kuma karin bayanin da ya yi wa Yusuf Ibrahim Yakasai a wata hirar da suka yi kan batun.