Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'An kama magoya bayan PDP fiye da 300 a Bauchi'
Ku latsa hoton sama domin sauraren hirar Is'haq Khalid da Sanata Bala Muhammad.
Dan takarar babbar jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya, Sanata Bala Muhammad Kaura, ya yi zargin cewa 'yan sanda sun kama magoya bayansa fiye da 300 a cikin jihar.
Jam'iyyar ta PDP ta yi wannan zargi ne a wani taron manema labarai da ta gudanar a birnin Bauchi a ranar Alhamis.
Dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP Sanata Bala Muhammad wanda shi ne babban mai kalubalantar gwamnan jihar, Muhammad Abdullahi Abubakar, na jam'iyyar APC wanda ke neman wa'adi na biyu ya shaida wa Is'haq Khalid cewa an fara kama magoya bayan nasu ne tun kimanin makwanni biyu da suka gabata kuma ana ci gaba da kamen.
Ya yi zargin cewa ana tsare da magoya bayan jam'iyyarsu ta PDP, yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamna da na 'yan majalisar dokokin jiha.
Zuwa yanzu rundunar 'yan sandan jihar ba ta ce komai ba game da zargin, amma kwamishinan watsa labarai na jihar Bauchi, Umar Muhammad Sade, ya musanta zargin, yana mai cewa duk wanda jami'an tsaro suka kama, mutum ne da ake zargi da aikata laifi.
"Yan adawar na shure-shure ne kawai," in ji shi.
'Yan adawar na zargin cewa jami'an tsaro da gwamnatin jam'iyyar APC da ke mulki a jihar da hada baki domin musguna masu.