Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda jami'an tsaron Sudan ke murkushe masu zanga-zanga
Latsa hoton sama domin kallon bidiyon da gwamnatin Sudan ba ta son a gani
Wasu hotunan bidiyo da masu zanga-zanga suka dauka ya nuna yadda jami'an tsaro ke farautar masu zanga-zanga a titunan birnin Khartoum.
Bidiyon ya nuna yadda dakarun suke duka da tsare masu zanga-zanga a wani wuri na sirri ba tare da an kai su kotu ba.
Su wa ye su? Ina ake tsare su? Ya ya suke aiki?
Wasu daga cikin wadanda suka tsira sun fada mana cewa akwai wani firji a ginin da ake amfani da shi wajen azabtar da mutane.