INEC ta kara wa'adin karbar katin zabe

Shugaban INEC

Asalin hoton, @inecnigeria

Lokacin karatu: Minti 1

Hukumar zabe a Najeriya INEC ta sanar da kara lokacin raba katin zabe bayan wa'adin da ta diba tun da farko ya cika.

Shugaban hukumar INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da kara wa'adin rarraba katinan zaben daga yau juma'a zuwa litinin 11 ga watan Fabrairu.

Karin na kwana uku ya kunshi har da ranakun Asabar da Lahadi.

INEC ta ce ta kara wa'adin ne bayan kiranye-kiranyen da ta samu na neman a kara wa'adin raba katinan zaben.

A baya dai hukumar ta ce akwai miliyoyin katunan zaben da masu su ba su je sun karba ba.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP na cikin jam'iyyun siyasa da suka nemi a kara lokacin rarraba katinan zaben.

Akwai daruruwan 'yan Najeriya da ba su karbi katinsu na zabe ba, kuma hukumar zaben kasar ta ce duk wanda bai karbi katin ba zai yi zabe ba.

Hukumar zaben kasar kuma ta ce bayan wa'adin da ta diba ya kawo karshe a ranar Litinin 11 ga Fabrairu, za ta mika ajiyar katinan zaben da ba karba zuwa Babban Bankin Najeriya har sai an kammala zabe inda za a ci gaba da rijista da kuma raba katinan.