Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Watsa min acid ya kara min kwarin gwiwa ne – Nura M Inuwa
- Latsa alamar lasifika da ke hoton da ke sama don kallon cikakken bidiyon
Shahararren mawakin fina-finan Hausa nan, Nura M Inuwa, ya bayyana wa BBC yadda ya samu kwarin gwiwa bayan da aka watsa masa acid.
Mawakin ya bayyana hakan ne a wata hirar musamman da ya yi da BBC a kwanakin baya.
Nura ya ce abin da ya same shin ya kara masa son jama'a ne, maimakon gudun su.