Ashe ba a sukar Saudiyya a kwana lafiya?

Bayanan bidiyo, Bidiyon yadda masu sukar Saudiyya ke batan dabo.

Latsa alamar hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Saudiyya ta amince cewa an kashe dan jarida Jamal Khashoggi a ofishin jakadancinta da ke Santanbul, mun yi duba kan sauran masu sukar lamirin Saudiyya da sukai batan dabo.

Ana kara matsa wa Saudiyya lamba kan ta yi cikakken bayani kan makomar dan jaridar.

An yi wa Khasoggi ganin karshe a ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Santabul na Turkiya fiye da makonni biyu da suka gabata.