Kwankwaso ya kaddamar da takararsa a zaben 2019

Tsohon Gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da takarar neman shugabancin Najeriya a babban zaben shekarar 2019.

Dan siyasar ya kaddamar da aniyyar hakan ne a wani filin taro da ke unguwar Jabi a Abuja ranar Laraba.

Sai dai gabanin hakan, a ranar Talata wani jigo a kwamitin yakin neman zaben Sanata Kwanwaso, Kwamred Aminu Abdussalam, ya yi ikirarin cewa hukumomi sun hana tsohon gwamnan jihar Kano din taron siyasa a wurare biyu a Abuja.

Dubban magoya bayan dan siyasar ne suka taru a dandalin da ya bayyana aniyyarsa ta neman tsayawa takarar.

Kwankwaso na cikin mutane da dama da ke son PDP ta tatsayar da su takara domin fafatawa da Buhari a 2019.

Ba wannan ne karon farko dan tsohon gwamnan yake neman shugabancin kasar ba.

Ya fara neman takarar ne a zaben 2015, sai dai ya sha kaye a hannun Shugaba Muhammadu Buhari bayan zaben fidda gwani na jam'iyyar APC.

A cikin watan Yuli ne Sanata Kwankwaso da shugaban Majalisar Dattawan kasar Bukola Saraki da wadansu gwamnoni da 'yan majalisa da dama suka bar APC zuwa PDP.

Tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa da ke neman PDP ta tsayar da shi takarar shugabancin kasa ya ce matakan da ya rike sun sa ya fi sauran masu neman takarar shugabanci a jam'iyyar cancanta.

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce cancanta ce ta sa shi fitowa neman takarar.

To sai dai Sanata Kwankwaso ya ki amsa wasu tambayoyi da BBC ta yi masa kan al'amuran siyasa, ciki har da batun alakarsa da gwamnan Kano Abduallahi Umar Gandaje. To amma ya ce nan gaba zai yi magana kan batutuwan.