Sai yaushe Dangote zai sayi Arsenal?

Shahararren attajirin nan Aliko Dangote ya jima da bayyana cewa yana so ya sayi kulob din Arsenal, sai dai ya ce a yanzu akwai wasu abubuwa da suka fi sayen Arsenal muhimmanci.

Dangote ya jima da nuna sha'awar sayen kulob din Arsenal, sai dai a yanzu ya ce kammala gina kamfanoninsa ne a gabansa.

Wakilin BBC Nasidi Adamu Yahaya ne ya tattauna da Aliko Dangote a Legas, kuma ya fara da tambayarsa ra'ayinsa kan matakin gwamnatin na yin amfani da kudaden China da yayin hulda da China, maimakon amfani da dalar Amurka.