Abiola mai tsoron Allah ne — Zainab Abiola

Tsohuwar matar marigayi Cif Moshood Abiola, mutumin da ake jin shi ne ya lashe zaben 12 ga watan Yunin 1993 a Najeriya, wato Zainab Duke Abiola ta shaida wa BBC irin halayensa da kuma irin abubuwan sa da ya yi a rayuwarsa wadanda za a iya tunawa da shi.

Zainab Abiola, ta yabi maigidan nata, tare da kuma da nuna farin cikinta da ma na sauran iyalansa a kan ayyana ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar dimokradiyya a Najeriya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ne ya ayyana ranar 12 ga watan Yunin a matsayin ranar dimokradiyya, mai makon ranar 29 ga watan Mayu da aka saba gudanar da bikin zagayowar ranar dimokradiyyar.

Ko da yake, gwamnatin kasar ta ce bikin ranar dimokradiyyar zai fara ne daga 12 ga watan Yunin shekarar 2019.

Duk da wasu jihohi a yankin Kudu maso yammacin Najeriyar sun ayyana ranar 12 ga watan Yunin na shekarar 2018, a matsayin ranar hutu, kuma ana sa ran bikin zai zo da wani irin sauyi don kuwa masu rajin tabbatar da ganin 12 ga watan Yuni ta kasance ranar dimokradiyya, za su fita ne don yin bukukuwa maimakon zanga-zanga da kiraye-kirayen da suka saba yi shekara da shekaru.