Za ki yarda a nuna hotonki don yi mi ki dalilin mijin aure?

Latsa hoton da ke sama don sauraron tattaunawar da Fatima Zahra Umar ta yi da Mai Dalilin Aure:

Malam Shu'aibu mai dalilin aure, wani bawan Allah ne da ke zaune a unguwar Dorayi Babba a birnin Kano, wanda ke yi wa mutane hanyar nema musu miji ko mata don yin aure.

Watakila yana iya zama shi ne babban Mai Dalilin Aure a jihar Kano. Tun shekarar 1998 yake yi wa mutane dalilin aure ta hanyar samar musu miji ko mata, kuma har yau ba ta sauya zani ba.

Yana samun yabo da jinjina sosai kuma shi ne Shugaban Kungiyar Masu Dalilin Aure ta jihar Kano.

Na ziyarce shi a ofishinsa domin jin ta bakinsa kan wannan harka ta yin dalilin aure.

Ya ce matakan da yake bi masu sauki ne, abun da kawai yake bukata shi ne ya yi nazari kan mutumin da ya je masa da bukata don sanin irin miji ko wacce irin mata za ta da ce da shi.

Ya shaida min cewa kwarewarsa a aikin gadi ta sa kallo daya zai yi wa mutum ya gane halayyarsa.

Naira 2000 kawai ake biya domin a tattauna da shi kan irin abun da ake bukata.

Bayan wannan kuma ya kan bukaci a ba shi hoto da adireshin gida (wanda yake bincike a kai da kansa) da kuma lambar waya.

Ya kuma gaya min cewa yana iya nemar wa mace miji cikin kwana biyu kacal, amma ya danganta da irin yadda aka zaku da bukatar.

A takaice ma dai a gaggauce ya yarda muka yi hira saboda yana sauri zai je wani daurin aure wanda shi ya yi sanadin hada ma'auratan kwana bakwai kafin nan.

Shin za ki ko za ka iya auren maji ko matar da kuka hadu cikin mako daya kacal?