Yadda aka daura auren Yarima Harry da Meghan Markle
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon bikin kai tsaye:
Auren Yarima Harry da Meghan Markle a masarautar Birtaniya, auren da ake kira na shekara.
Daruruwan mutane ne suka halarci Windsor domin kallon bikin auren, yayin da miliyoyin mutane a sassan duniya suka kalli bikin kai-tsaye.
Shugaban Cocin Ingila, Archbishop na Canterbury, Justin Welby ne ya daura auren Yarima Harry da Markle da misalin 12 na ranar Asabar.
An gudanar da bikin auren ba tare da mahaifin Amarya ba, Thomas Markle, saboda yana jinyar rashin lafiya.
Yarima Charles ne ya raka amarya a wajen daurin auren a madadin mahaifinta.
An daura wa Yerima Harry da Meghan Markle aure a cocin St. George da ke Windsor, inda nan ne aka daura auren Yerima Peter Philips da Autumn Kelly a shekarar 2008.
Mutune 600 aka tura wa goron gayyata, kuma an tura wa karin mutane 200 da goron gayyata domin halartar liyafar cin abincin da aka shirya wa ango da amaryarsa da za a yi a da yamma, ciki har da Spice Girls, da suka yi fice a fagen waka.
Sai dai daga cikin wadanda aka gayyata babu shugaban Amurka Donald Trump da tsohon shugaban kasa Barack Obama da matarsa duk da abokan Yarima ne.