'Ni mata-maza ne amma na fi son zama namiji'

Mata-maza wasu mutane ne da aka halicce su da al'aurar maza da ta mata, ko da yake saboda karancinsu a tsakanin al'umma ba kowa ne ke ganinsu ba.

A wasu sassa na duniya dai, musamman ma a kasashen Afirka, wadannan mutane kan fuskanci tsangwama da kyara.

Halima Umar Sale ta hadu da wani mata-maza wanda ya shaida mata cewa tun da ya fara wayo ya fahimci halin da yake ciki.

Don haka ta tambaye shi ko yaya aka rika kallon shi a lokacin?