Zaben Malaysia: Mai shekara 92 ya lashe zaben shugaban kasa

Asalin hoton, AFP
Tsohon firai ministan Malaysia, Mahathir Mohamad mai shekaru 92 ya bada mamaki bayan ya kayar da jam'iyyar da ta mulki kasar na tsawon shekara 60 a zaben shugabancin kasar.
Hukumar zaben kasar ta ce hadakar jam'iyyun siyasa na Mista Mahathir sun lashe kujeru 115, wanda ya zarce 112 da suke bukata domin kafa gwamnati.
Mista Mahathir mai shekara 92 ya kada jam'iyya mai mulki ta Barisan Nasional wadda ta shafe fiye da shekara 60 tana kan mulki.
Ya dade da yin ritaya, amma saboda zaben ya dawo domin karawa da tsohon yaronsa a siyasa, Najib Razak.
"Ba mun zo ramuwa ba ne, so muke mu dawo da doka da oda," inji Mista Mahathir.
Karanta karin wasu labaran
Ya kuma ce yana fatan za a gudanar da bikin rantsar da shi ranar Alhamis, wanda zai mayar da shi shugaban kasa mafi yawan shekaru a duniya.
Saboda wannan nasarar, an bayyana ranakun Alhamis da Jumma'a a matsayin hutu a fadin kasar.

Asalin hoton, AFP
Wannan yakin neman zaben ya hada Mista Mahathir da tsohon yaronsa na siyasa, wato firayi minista mai ci Najib Razak.

Asalin hoton, Getty Images











